1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Karuwar gangamin goyon bayan Falasdinawa a jami'o'in Amurka

May 3, 2024

Daliban jami'o'in Amurka na ci gaba da zanga-zangar bukatar kawo karshen yakin Gaza da yin kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Biden da manufofinta a kan Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4fToN
Hoto: Caitlin Ochs/REUTERS

An kama dalibai fiye da 2000 a cikin kusan makwanni uku da fara zangar-zangar a jami'o'in da suka hada da na California  da Taxes da Columbia. Umar Sheik Dahiru Bauchi, dalibi ne mai yin karatun digirin-digirgir, watau PhD a Columbiya, jami'ar da ta fara aza tubalin wannan lamari, da ya ke fantsama kamar wuta daji, wanda ya yi bayani a kan gundarin bukace-bukacen daliban.

USA New York City  | pro-palästinenische Proteste an Universität
Hoto: Caitlin Ochs/REUTERS

Koda yake ana ci gaba da yin tir da matakan karfin da 'yan sanda suke dauka, amma magajin garin New York, Eric Adams ya ce, ba zai zuba idanu wasu bata-gari su canja akalar zanga-zangarzuwa tarzoma ba, yana mai cewa, wani rahoton sirri, ya nuna masa cewa kashi 40 cikin 100 na 'yan zanga-zangar ba daliban Columbia ba ne.

Shugabar Jami'ar Brunswick, da ke jihar New Jersey, Farfesa Francine Conway, ta kara da cewa, da wajewar da suka yi da daliban, ta kara bude kofar ci gaba da tattaunawa tare da duba korafe-korafen daliban, musanman Larabawa da Musulmi da Falasdinawa su fiye da dubu bakwai a jami'arta.

USA Atlanta | pro-palästinenische Proteste an Universität
Hoto: Elijah Nouvelage/AFP/Getty Images

Amma a jami'ar Taxes da ke Dallas, labari ya sha bambam, domin kuwa a can ma sai da 'yan sanda suka yi amfani da karfi wajen korar dalibai daga sansanin da suka yi cikin Jami'ar. Wata daliba mai suna Nidaat, ta yi tir da gwamnatin Texas da hukumomin Jami'ar a kan irin matakan da suka dauka da suka ce 'yancin da doka ta ba su.

A halin da ake ciki dai, Jami'an 'yan sanda a jihohi dabam-dabam, sun yi biris da gaiyatar da wasu Jami'oin suka yi musu, na su kawo dauki, domin korar daliban da suka yi zaman dirshan. Suka ce, daukar wannan mataki, tamkar ingiza mai kantu ruwa ne.