1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar goyon bayan Odinga

Ramatu Garba Baba
March 20, 2023

Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai saka kwalla wajen tarwatsa dandazon magoya bayan madugun adawa Raila Odinga da ke ikirarin lashe zaben kasar na bara.

https://p.dw.com/p/4OwVf
Masu zanga-zangar adawa da shugaba Williams Ruto
Masu zanga-zangar adawa da shugaba Williams RutoHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Yan sanda a kasar Kenya sun yi amfani da hayaki mai saka kwalla wajen tarwatsa dandazon magoya bayan madugun adawan kasar Raila Odinga, jami'an tsaro dai sun tilasta wa Mista Odinga barin harabar wani Otel da ke Nairobi babban birnin kasar, in da ya shirya wata gana wa da manema labarai, kan abin da ya kira kwace nasarar da ya yi a zaben kasar na watan Agustan bara, da hukumar zabe ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

Rahotanni daga kasar da ta sha fama da rikicin bayan zabe, sun nunar da cewa, an yi arangama a tsakanin masu zanga-zangar goyon bayan Odinga a wani yanki da ake da dimbin magoya bayan madugun adawan da jami'an 'yan sanda.