1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Ambaliyar ruwa ta tagayyara mutane 470,000

May 10, 2024

Hukumar Abinci ta Duniya, WFP ta ce iftila'in ambaliyar ruwa a gabashin Kwango ya jefa rayukan mutane fiye da 470,000 cikin mawuyacin hali.

https://p.dw.com/p/4fiCj
Hukumar WFP  ta ce ambaliyar ruwa a Kwango ta jefa mutane 470,000 cikin wani hali.
Hoto: GLODY MURHABAZI/AFP

Hukumar Abinci ta Duniya WFP ta ce wadanda ambaliyar ta rutsa da su a kwango na fuskatar hadarin kamuwa da cututtuka saboda ba su da zabin da ya wuce wanke kaya sakawansu da kuma kwanuka da gurbataccen ruwa.

Hukumar ta kuma kara da cewa a yanzu bata da isasshen wadatar da za ta kai dauki ga wadanda iftila'in ya rutsa da su.

Karin bayani:Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane sama da 60 a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango

Mamakon ruwan sama da aka rika tafkawa a karshen shekarar bara a kasar ya haifar da tumbatsar rafuka a kudancin lardunan Kivu da Tanganyika da lalacewar amfanin gona da kuma hanyoyi wanda ya tilastawa wasu kauyawan neman mafaka a wasu wuraren.