1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mulkin mallaka: Sarkin Ashanti ya baje kolin kayan tarihi

May 1, 2024

A karon farko, Sarkin Ashanti na kasar Ghana ya baje tarin kayan tarihi na alfarma da turawan mulkin mallaka suka wawushe, bayan an ba da aron su karkashin wata yarjejeniya da masarautar ta kulla da Burtaniya.

https://p.dw.com/p/4fPID
Bikin baje kolin kayan tarin da turawan mulkin mallaka suka wawushe a Ghana
Bikin baje kolin kayan tarin da turawan mulkin mallaka suka wawushe a GhanaHoto: Christian Thompson/Matrix Images/picture alliance

Sarkin Ashanti Otumfuo Osei Tutu II ya tsara bikin baje kolin kayayyakin tarihin ne a fadar Manhyia da ke birnin Kumasi, domin tunawa da dakarun Ashanti da suka kwanta dama a lokacin yaki da mulkin mallaka a 1874.

Karin bayani: Ghana ta bukaci hadin kai don neman diyyar mulkin mallaka 

Tun da farko gidajen adana kayan tarihin Burtaniya ciki har da ''British Museum'' sun amince da mika takubban zinare 32 da wasu kayayyakin na alfarma ga masarautar ta Ashanti.

 

Tarihin Yaa Nana Asantewaa

Baje kolin kayayyakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai da Amurka ciki har da Faransa da Jamus da Portugal ke fuskantar matsin lamba na dawo da kayan tarihin da suka wawushe a lokacin mulkin mallaka.