1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taiwan ta kabalanci Chaina

Suleiman Babayo
January 2, 2019

Shugabar kasar Taiwan ta yi watsi jawabin shugaban Chaina na sake hade kasashen biyu ko da karfi idan haka ya zama tilas.

https://p.dw.com/p/3Av56
Xi Jinping Rede Taiwan
Hoto: Reuters/M. Schiefelbein

Shugaba Tsai Ing-wen ta kasar Taiwan ta yi watsi da kalaman Shugaba Xi Jinping na Chaina kan amfani da karfi wajen hade Taiwan da Chaina idan haka ya zama tilas. Shugaban Xi ya ce kasarsa ba za ta yanke kauna ba a game da yiwuwar yin amfani da karfi wajen yakar gwamnatin 'yan awaren yankin Taiwan tare da shan alwashin sake hade kasar ta Chaina a wuri daya.

A shekarar 1949 Taiwan ta balle daga Chaina sakamakon yakin basasa. Kuma Shugaba  ta Taiwan ta ce ba za su amince da amfani da karfi ba kan sake hade Chaina kasa guda tare da Taiwan. Sannan Taiwan ta zargi Chaina da watsi da yarjejeniyar da aka cimma na bangarori masu amfani da tsari dabam-dabam.