1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben Chadi 2024: Tarihin Lydie Beassemda ta jam'iyyar PDI

April 30, 2024

Daga cikin 'yan takara 10 da za su fafata a zaben shugaban kasar Chadi a ranar 6 ga watan Mayun 2024, akwai 'yar takara mace daya tilo Lydie Beassemda ta jam'iyyar PDI

https://p.dw.com/p/4fM0w
Lydie Beassemda, 'Yar taakarar shugabar kasa a Chadi
Lydie Beassemda, 'Yar taakarar shugabar kasa a ChadiHoto: Privat

Mai shekaru 57, Lydie Beassemda, injiniya ce a masana'antar abinci. Ta na da digiri a kimiyyar dabi'a da kuma digiri a fannin ayyukan gona. Digirorin da ta samu a jami'o'in Chadi, da Nijar, da Burkina Faso da Jami'ar Quebec da ke Montreal.

Ta kasance ministar da ke kula da al'amuran noma daga shekarar 2018 zuwa Agusta na shekarar 2019, kafin a nada ta ministar ilimi mai zurfi a gwamnatin rikon kwarya a watan Mayu na shekarar 2021, wadda majalisar mulkin soji ta kafa.

Lydie Beassemda 'yar takara shugabar kasa a Chadi
Lydie Beassemda 'yar takara shugabar kasa a ChadiHoto: Privat

Lydie Beassemda ta shiga siyasa a karon farko a watan Afrilun shekarar 2010, a gungun mahaifinta, Djébaret Julien Beassemda, shugaban jam'iyyar da ake kira "Parti pour la démocratie et l'indépendance intégrale PDI. Jam'iyyar da ke goyon bayan tsarin tarayya, wanda ya kafa a 1997.

"Ta ce na shiga harkar siyasa ne domin goya wa mahaifana baya, wadanda suka dukufa cikin siyasa, na yi niya na bada taimako ga wadanda na ke gani sun gaji kuma sun dade suna ci gaba da gwagwarrmaya"

Bayan rasuwar mahaifinta a shekarar 2018, Lydie Beassemda ta karbi ragamar shugabancin jam'iyyar PDI wadda ta kasance babbar sakatariyar jam'iyyar tun a shekarar 2014. A gareta, wa'adin zabe wata dama ce a gareta na samun horo kan siyasarta.

Yakin neman zaben shugaban kasa a Chadi
Yakin neman zaben shugaban kasa a ChadiHoto: Idriss Deby Itno/Facebook

"Wata dama ce a garemu, mu kara tabo batun tarayya, abubuwan da ke bamu karfin gwiwa a duk abin da muke yi shi ne tarayya."

Kan batun taka birki da mata ke fuskantar a harkokin siyasa, Lydie Beassemda ta soki yadda maza ke kin raba madafun iko.

"Har yanzu mukaman siyasa ba su da karfi a kasar Chadi, idan aka samu matsaloli, abokan siyasarmu sun fi son ciwo kansu a tsakaninsu, ba sa yarda mata su halarci taron yanke shawarwari a fagen siyasa, amma, wasun mu, mun samu tarbiyar cewa shi hakkin ba shi da jinsi."

Yakin neman zaben shugaban kasa a Chadi
Yakin neman zaben shugaban kasa a ChadiHoto: Idriss Deby Itno/Facebook

Mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin kasar Chadi, ta zo ta uku a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Afrilun 2021, inda ta samu kashi 3.16% na kuri'un da aka kada. Duk da karancin wannan makin, Lydie Beassemda ta yi imanin nasara a wannan karon, a ranar 6 ga Mayu, kuma ta bayyana abubuwan da ta fi bai wa fifiko.

"Ayyukan mu na zamantakewa yana bukatar hangen nesa na maida kasar Chadi wata kasa mai karfi da aka kafa a cikin tarayya da samun daidaiton 'yancin, inda za a iya samun dama ga komi."

Lydie Beassemda, mace ce mai fafutukar kare hakkin bil'adama, musamman kan harkokin mata.

Ta na tsaye tsayin daka kan yaki da talauci, inganta jinsi da raya karkara. A gareta, ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na yiwuwa ne da gudunmawar jama'a cikin harkokin mulki yadda ya kamata.